Rundunar sojin Algeria ta harbe wasu ƴan kasar Morocco biyu da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi zuwa kasar, sanarwa daga ma’aikatar tsaro ta fita a jiya Asabar tace, mako guda bayan da shugaban Kasar Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya sanar da daukar tsauraran matakai kan safarar miyagun kwayoyi daga kasashen waje.
Abdelmadjid Tebboune ya yi barazanar daukar mataki kusan mako daya da ya gabata kan masana’antu da ke samar da miyagun kwayoyi, a daidai lokacin da ake ci gaba da zargin cewa makwabciyar kasar Morocco wato Algiers ta yanke huldar diflomasiyya da ita a shekarar 2021 ita ce ke da hannu a safarar miyagun kwayoyi zuwa kasar.
Ma’aikatar tsaro ta bayyana cewa wadanda ake zargin masu safarar miyagun kwayoyi biyu, sun bijerewa umarnin soji na su tsaya a bicinke su, kafin a kashe su. Ba a fayyace ko mutanen biyu suna da makamai ba.
Babu wata sanarwa daga bangaren hukumomin Morocco.
A wata sanarwa, ma’aikatar ta bayar da rahoton kama wasu mutane 17 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi da kuma kwace tarin sinadarin wiwi da suka fito daga Morocco.