Sojojin kasar Yemen sun kaddamar da sabbin hare haren maida martani kan barikokin sojoji da kuma cibiyoyin arzikin man fetur na kasar Saudiya a jiya Lahadi, a yunkurin da take yi na kwato yankunan yammacin kasar daga mamayar saudia.
Tashar talabijan ta Presstv a nan tehran ta nakalto majiyar gwamnatin Yemen na cewa makamai masu linzami samfurin Bilistic da wasu tarin Drones sun fada a kan wurare a yankunan Khmis, Mashait, Najran, Jizan da kuma Abha na kasar Saudia, saboda kawo karshen killacewar da kasar take ci gaba da yiwa mutanen kasar Yemen fiye da shekaru 12 da suka gabata.
Labarin ya kara da cewa hare hare sun sauka a kan cibiyoyin mai na Aramco, barikokin sojoji da kuma tashoshin jiragen saman yaki a cikin kasar. Tace makaman sun lalata wurare da dama kuma gobara sun tashi ana iya ganin hayaki na tsahi a cibiyoyin Aramco da dama.
Labarin yakara da cewa, sojojin saudia da dama sun ji rauni a iya abinda suka sani ya zuwa lokacin bada wannan labarin. Sannan wasu sabbin hare hare sun fada a kan Sharurah a cikin Lardin Najran.
Wannan duk suna zuwa ne bayan hare hare kimani 100 wadanda jiragen yakin saudia suka kai kan wurare daban daban a cikin kasar ta Yemen.