Saudiyya Ta Sanar Da Gano Ma’adanin “Uranium” Fiye Da Ton Miliyan 110 A Birnin Madina Mai Tsarki

Ministan Makamashi na kasar Saudiyya Abdulaziz Bin Salman ne ya sanar da gano ma’adanin Urani’um din a yayin wani taro na hukumar makamashin Nukiliya ta

An gano Sanadarin Uranium

Ministan Makamashi na kasar Saudiyya Abdulaziz Bin Salman ne ya sanar da gano ma’adanin Urani’um din a yayin wani taro na hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa a birnin Geneva.

Dama dai a cikin watan Yuli ne hukumar makamashi ta kasa da kasa dake karkashin MDD, ta sanar da masaniyarta akan Shirin da Saudiyya da Amurka suke da shi na aiki tare a fagen fasahar makamashin Nukiya.

Sai dai kuma daga bayan shugaban kasar Amurka Donadl Trump ya yi amai ya lashe, inda  ya bayyana cewa aiwatar da yarjejeniyar da kasarsa ta kulla da Saudiyya zai kasance ne bisa sharadin Riyadh ta kulla alaka da Isra’ila.

Ita ma ma’aikatar makamashin na Amruka ta sanar da cimma yarjejeniyar da Saudiyya wacce ta kimarta ta biliyoyin daloli ce.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted