Tsohon jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Harin 11/09 kan Amurka ya zame dalilin bude fagen yake-yaken Amurka a duniya
Wani tsohon jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya yi ikirarin cewa: “Yaki da ta’addanci” da Amurka ke jagoranta ba wai kawai ya gaza raunana kungiyoyin ‘yan ta’adda ba ne, har ma ya taimaka wajen samar da yanayi na bullar wasu kungiyoyin ‘yan ta’addan a duniya kamar ISIS.
Alfred de Zayas, kwararre kan kare hakkin dan adam, farfesa a fannin shari’a, kuma tsohon jami’in Majalisar Dinkin Duniya, ya bayyana a wata hira da kamfanin dillancin labarai na ISNA cewa: Hare-haren 11 ga watan Satumba sun haifar da mummunan sakamako a siyasa, tsaro, da kuma fannin siyasa. Ya bayyana cewa yakin da Amurka ke jagoranta kan ta’addanci bai raunana kungiyoyin ‘yan ta’adda ba, amma ya samar da yanayi na bullar Karin wasu kungiyoyin kamar ISIS.
Tsohon kwararre mai zaman kansa na Majalisar Dinkin Duniya kan inganta tsarin dimokuradiyya da adalci na kasa da kasa ya yi jayayya cewa manufofin mulkin mallaka na Amurka da kungiyar Tsaro ta NATO su ne tushen ta’addanci. Ya kara da cewa an yi amfani da hare-haren ranar 11 ga Satumba a matsayin kayan aiki don takaita hakkokin dan adam a Amurka da kuma kare yaƙe-yaƙenta.