Iran Zata Fito Da Sabbin Dabarbarun Yaki Idan An Sake Takalarta

Ministan tsaro na rki a nan kasar Iran ya bayyana cewa idan wani yaki ya sake barkewa tsakanin Iran da Amurka makiya zasu yi mamaki,

Ministan tsaro na rki a nan kasar Iran ya bayyana cewa idan wani yaki ya sake barkewa tsakanin Iran da Amurka makiya zasu yi mamaki, saboda sojojin Iran zasu sake fitowa a wannan karon ma da sabbin ci gaba a kayakin yakin wadanda makiya basu taba ganin iransu ba. Haka ma barnan da zasu yi sai ya wuce na baya nesa ba kusa ba.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Burgediya Janar Majid Ibn Reza yana fadar haka a lokacinda yake ganawa da  shugaban kamfanonin makamai na kasar Iran a jiya Lahadi. Ya kuma kara da cewa wasu jami’an gwamnatin Amurka suna ganin har yanzun suna iya sauya ra’ayin Iran su kuma tursasa mata mika kai ga bukatunsu. Wanda wannan babban kuskure ne sai kuma sun gwada zasu fahinci hakan.

Ya ce har yanzun akwai wasu jami’an gwamnatin Amurka suna barazanar sake komawa yaki da Iran, a zatonsu a wannan karon zasu sami nasara a kanta. Ya ce abunda suke tunani ba wani abu ba in banda kuskuren lissafi, kuma zasu yi nadama ne kawai bayan sun tapka wani kuskure.

Ibn Reza ya kara da cewa idan suna da hankali yakamata su san yanda zasu yi magana da JMI. Su san cewa daga yanzun it aba kawwan lasa ba ce.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted