Iran: Kungiyoyin “Brics” Da Shanghai Sun Nuna Kin Amincewarsu Da  Kakaba Takunkumin Amurka Na Gefe Daya

Iran: Kungiyoyin "Brics" Da Shanghai Sun Nuna Kin Amincewarsu Da Kakaba Takunkumin Amurka Na Gefe Daya
baka'i yana taron manema labari

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar musulunci ta Iran Dr. Isma’ila Baka’i ya bayyana cewa; Mambobin Kungiyoyin na Brics da kawancen Shanghai suna yi aiki da dukkanin abinda za su iya wajen kalubalantar takunkumin Amurka na gefe daya, da kuma nemo hanyoyin dakile tasirinsa.

Dr. Baka’i wanda ya gabatar da taron manema labaru a yau Litinin ya yi watsi da mafarkin Amurka akan cewa za a mayar da Iran saniyar ware, yana mai kara da cewa; kasar da ta iya kare kanta, kuma take samun yabo daga kasashen duniya, babu yadda za a iya killace ta da mayar da ita saniyar ware.

Haka nan kuma kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya yi Ishara da yadda kimar Amurka da kwarjininta ya zube warwas bayan harin da ta kawo wa Iran tare da Haramtacciyar Kasar Isra’ila.

Dr. Baka’i ya ce; Kungiyoyin kasa da kasa da su ka hada da kasashen wannan yankin, sun yarda da cewa Amurka ta take dokokin kasa da kasa sannan kuma ta jefa zaman lafiya da tsaron duniya cikin hatsari.

Kuma hatta kawayen Amurka na kusa da su ka hada Canada da turai sun yarda da cewa; Da akwai bukatar a kalubalanci Halayyar Amurka ta barna a fagen siyasar kasa da kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted