Pezeshkian: Akwai Muhimmancin Inganta Tsarin Hadin Gwiwa

Shugaban kasar Iran ya jaddada muhimmancin inganta tsarin haɗin gwiwa tsakanin ɓangarori daban-daban da kuma cinikayyar kuɗaɗen ƙasashen duniya, da kuma rashin iyawar Amurka na

Shugaban kasar Iran ya jaddada muhimmancin inganta tsarin haɗin gwiwa tsakanin ɓangarori daban-daban da kuma cinikayyar kuɗaɗen ƙasashen duniya, da kuma rashin iyawar Amurka na aiwatar da manufofin mulkin mallaka

Shugaban kasar Iran Mas’oud Pezeshkian ya bayyana cewa: Sanarwar ƙarshe ta taron kungiyar BRICS ta haɗa da yin Allah wadai da hare-haren da aka kai wa cibiyoyin fararen hula, goyon bayan shigar Iran cikin Ƙungiyar Kasuwanci ta Duniya, mai da hankali kan cinikin kuɗaɗen ƙasa, da kuma adawa da takunkumin da aka kakaba wa Iran na ɓangar guda. Ya jaddada cewa: “Dukkan ƙoƙarin Iran ya mayar da hankali ne kan gabatar da matsayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da manufofin taron, waɗanda suka haɗa da sassauci, kirkire-kirkire, haɗin gwiwa, da dorewa, yayin da aka gudanar da tattaunawa mai kyau tsakanin shugabannin ƙasashen da suka shiga taron.”

A ranar Lahadi, a ƙarshen halartarsa ​​a taron kungiyar BRICS karo na 18 da aka yi a New Delhi na Indiya, Shugaban Iran ya yi magana game da taron da ya haɗa membobin kungiyar BRICS da ƙasashen da suka nemi shiga ƙungiyar. Ya bayyana cewa “akwai mambobi 11 na kungiyar BRICS, yayin da wasu ƙasashe 10 suka gabatar da buƙatun shiga ƙungiyar, kuma an gudanar da tattaunawa mai kyau a taron haɗin gwiwa da waɗannan ƙasashe.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted