Baqa’i: Iran Tana Kai Hare-Hare Ne Kawai Kan Sansanonin Amurka

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Sojojin Iran sun kai hare-hare kan sansanonin Amurka wadanda su ne tushen kai hare-haren ta’addanci kan Iran

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Sojojin Iran sun kai hare-hare kan sansanonin Amurka wadanda su ne tushen kai hare-haren ta’addanci kan Iran

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Isma’il Baqa’i ya tabbatar da cewa: Kowane makami mai linzami na Amurka da ta kai hari kan zauren wasanni da ke Lamerd ya ƙunshi gutsuttsura 180,000.

Baqa’i ya shaida wa tashar tlabijin ta Al-Mayadeen cewa: “Sakon Iran ga ƙasashen yankin shi ne cewa: Iran ba ta kai hari ga waɗannan ƙasashe ba, sai dai sansanonin Amurka da suka kasance tushen kai hare-haren wuce gona da iri kan Iran.”

Ya ƙara da cewa: Taron da aka shirya gudanarwa a Oman a ranar Litinin zai zama muhimmin mataki na tabbatar da kwanciyar hankali da tsaro a yankin Tekun Pasha.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted