Kungiyar ta malaman musulunci na duniya ta bayyana cewa: Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suna ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wutar yaki a Gaza, da kuma yankin yammacin Kogin Jordan, kuma ‘yan’uwanmu suna ci gaba da fuskantar kai hare-hare da jefa su cikin tsoro.
Haka nan kuma kungiyar ta malaman musulunci ta duniya ta jaddada cewa, ci gaba da keta tsagaita wuta ya sa ana kai wa Falasdinawa hare-hare da jefa su cikin tsoro da tilasta musu yin hijira a kodayaushe.
A karshe kungiyar ta malaman musulunci ta ce wajibi ne ga al’ummar musulmi da dukkanin ‘yantattun a duniya da su kokarin ganin cewa wannan mummunan yanayin da mutanen na Gaza suke ciki bai zama wanda aka saba da shi ba ana kallo.