Araqchi: Iran Zata Yi Zaman Taro Da Kasashen Larabawa

Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Iran zata gabatar da sabbin taswirar hanya a mashigar Hormuz a taron Salalah gobe. Ministan Harkokin Wajen kasar

Ministan Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Iran zata gabatar da sabbin taswirar hanya a mashigar Hormuz a taron Salalah gobe.

Ministan Harkokin Wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya sanar a ranar Lahadi cewa: An shirya gudanar da wani taro a ranar Litinin a garin Salalah na kasar Oman, tare da halartar kasashe biyar na Majalisar Hadin Kan Kasashen Larabawan yankin tekun Pasha ta (GCC), wadanda suka hada da Iran da Iraki. Ya lura cewa taron zai yi wa kasashen da suka shiga bayani kan sabbin yarjejeniyar hanyar ruwa da aka cimma tsakanin Iran da Oman.

A wata hira da ya yi da kafar watsa labarai ta Al-Araby Al-Jadeed, Araqchi ya bayyana cewa: Taron zai iya, idan akwai wa’adin siyasa, ya share fagen tattaunawa a nan gaba kan wasu batutuwan da suka shafi yankin.

A karon farko, a tsakiyar rikicin da ke ci gaba da faruwa a yankin, za a gudanar da taron hadin gwiwa tsakanin Iran, kasashen mambobi a Majalisar Hadin Kan Kasashen Larabawan yankin tekun Pasha ta GCC, da Iraki a kasar Oman a ranar Litinin. Mene ne babban batun ajandar, kuma mene ne sakonni da manufofin wannan taron? Ta yaya aka cimma wannan ra’ayi?

Araqchi ya bayyana cewa: Yana so ya fayyace wani muhimmin batu game da wannan taron. Yana cewa: Taro ne na ƙasashen yankin tekun Pasha guda takwas, amma Bahrain, saboda dalilan da ta bayyana, ta ƙi shiga cikinsa. Saboda haka, za a gudanar da taron tare da halartar ƙasashe bakwai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted