Belgium: An Kori Wata Malamar Makaranta Daga Aiki Saboda Ta Ki Cire Lullubi

A wannan Litinin din ne da gwamnatin yakin “Flanders” a kasar Belgium ta kori wata malamar makaranta mai suna Hadija Amajourd saboda ta suturta jikinta.

mace mai hijabi

A wannan Litinin din ne da gwamnatin yakin “Flanders” a kasar Belgium ta kori wata malamar makaranta mai suna Hadija Amajourd saboda ta suturta jikinta.

Ita dai malama Hadija Amajour ta fara aiki ne ne a makarantar musamman a Assenede tun a cikin shekarar 2022, kuma tun wancan lokacin ne take Sanya hijabi.

Kungiyar kwadago ta yankin ta ce za ta kalubalanci hukuncin korar Hadija a gaban kotun koli dake birnin Brussels,domin lamarin  yana cin karo da ‘yancin addini.

A yankin Flanders ta gabas, a kasar Belgium dai da akwai dokar da ta hana amfani da duk wani alami na addini a cikin makarantu,kamar yadda kafafen watsa labarun yankin su ka ambata.

Malama Hadija ta kalubalanci dokar da cewa; an yi ta ne saboda siyasa ba wai saboda nuna karkata zuwa ga wani addini ba, tana mai kara da cewa: “Babu wanda bai karkata zuwa ga wata Akida ba, domin duk wani malami da ya tsaya a gaban aji, to yana tare da akidar da ya yi imani da ita.”

Tun a farkon shekarar karatu ta bana ne aka fara aiki da dokar hana malamai da dalibai Sanya duk wani abu da zai nuna addininsu, ko kuma ra’ayinsu na siyasa a cikin wannan yankin na Flanders ta gabas.

A cikin watan Mayu wasu dalibai shida sun kalubalanci dokar a gaban majalisar kasar ta Belgium,amma aka yi watsi da karar da su ka shigar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted