kwamandan hafsan hafsohin sojin kasar iran major janaral Amir Hatami ya sanar da bada ladan kudi dala dubu 30 ga duk wanda ya samu nasarar kashewa ko kuma kama sojojin Amurka, yace zamanin ci gaba da zaman sojojin Amurka a yankin tekun fasha ya zo karshe baki daya.
Da yake bayani a wajen taron girmama ranar yan jaridu ta kasa janar Hatami ya bayyana wani sabon shiri wanda ke samun goyon bayan gangami na tara kudade don tallafawa sojojin kasar dake ayyukan kare tsaron kasa, don haka bisa wannan shirin duk wanda ya samu kashe ko kama sojan Amurka tare da mika shi ga hukumomin da abin ya shafa za’a bashi ladan dala dubu 30, idan kuma mace ce ta to zaa ninka mata kudaden
Kaka zalika kwamandan yayi ishara da sabbin nade-nade da jagoran juyin musulunci na Iran yayi Ayatullah sayyid mujtaba Khamna’I na sabbin kwamadojojin soji da na tsaro har guda 6, ciki har da nadin babban kwamanda major janaral muhsin Rezeai a matsayin sabon sakataren majalisar kolin tsaron kasa
Da ya karkata game a mashigar Hurmuz kuma shugaban rundunar sojin ya bayyana hanyar ruwa mai muhimmanci a matsayin nasara da Allah ya bawa alummar iran na siyasa, yana mai tababtar da cewa ba za’ta sake komawa matsayinta na baya ba.