Jami’in tattara sakamakon zaben na hukumar zaben Najeriya INEC, Joshua Ogunwole, ya ayyana gwamnan kuma dan takara Adeleke na jam’iyyar Accord a matsayin wanda ya lashe zaben a hukumance a yau Lahadi a hedikwatar INEC da ke Osogbo, babban birnin jihar Osun.
Gwamnan ya samu jimillar kuri’u 511,067 yayin da abokin hamayyarsa na kusa, Bola Oyebamiji na APC, ya samu kuri’u 444,815.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce sake zaben gwamna Ademola Adeleke a karo na biyu, ya nuna cewar al’ummar Osun sun yadda dashi, yayin da ya bayyana sakamakon zaben a matsayin abinda ke alamta wanzuwar dimokradiyya a kasar.
Shi ma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar ya ce nasarar Adeleke ta nuna cewa al’ummar Osun sun zabi wanda suke so, a gefe guda dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC, Rabiu Kwankwaso ya ce wannan zabe tunatarwa ce ga al’umma, idan har suka jajirce zasu samu abinda suke so.