Iran Tayi Nasara A Bangaren Soji Da Siyasa A Yakinta Da Amurka Da HKI

kasar iran ta samu gagarumar nasara a yakinta da kasar Amurka da HKI

Mohammad Baqer Qalibaf shugaban majalisar shawarar musulunci ta Iran ya fadi cewa Iran ta samu gagarumar Nasara ta gaskiya a bangaren Soji da kuma bangaren siyasa a yakin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar a kanta domin dukkan bangarorin biyu ba su cimma koda daya daga cikin manufofinsu ba akan Tehran

Shugaban yayi  wannan maganar ce a wata ganawa da yayi da yan majalisar a jiya Asabar yace iran ta shagaltu da yakin rashin adalci da Amurka da isra’ila suka jagoranta akanta, ya kara da cewa alummar iran sun tsaya kyam sun yaki isra’ila da amurka na tsawon kwanaki 40, kuma sun taka muhimmiyar rawa wajen samun nasara a bangaren soji da na siyasa.

Babban jami’in ya jaddada cewa Amurka da isra’ila sun shiga yaki da iran ne da burin cimma wasu abubuwa guda 9 da suka sanar da su a hukumance, sai dai basu iya cimma ko da daya daga cikin ba, don haka wannan babban shan kaye ne ga Amurka da gwamnatin sahyuniya , amma iran ta samu nasara

Daga kare ya kara da cewa kasar Amurka da HKI sun kaddamar da Haramtaccen yakin kan kasar iran a ranar 28 ga watan fabareru sai dai bayan kwashen kwanaki 40 a ranar 8 ga watan Aprilu aka tilastama makiya amincewa da dakatar da bude wuta a daidai lokacin da iran take ci gaba da jajircewa wajen mayar da martani kan hare haren da ake kai mata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted