Sojojin Isra’ila Sun Harbi Falasdinawa A Yammacin Kogin Jodan.

ci gaba da kai hari da sojojin isra'ila ke kai wa a yankin gaza sun harbi wasu falasdinawa

Rahotanni da suka fito daga yankin falasdinusun sun nuna cewa sojojin Isra’ila da yahudawan yan share wurin zauna sun harbi falasdinawa tare dukan wasu da kuma tilasta musu barin gidajensu ba shiri,a wasu hare-hare da suka kai a gabatar yammacin kogin Jodan

Kungiyar bada agaji ta yankin falasdinu ta bayyana cewa a birnin Khalil an harbe wasu falasdinawa guda 2 tare da jikkata wasu guda 8 a wani hari da sojojin isra’ila suka kai a Al-jabari dake makwabtaka da garin arras

Wani bafalasdine dan shekaru 60 da haihuwa sojojin isra’ila sun harbe shi a baya da hannu, haka shi ma wani dan shekara 46 an harbe shi kafin a tsare shi, an bayyana cewa wasu mutane 8 ciki har da wata mata mai shekaru 66 sun ji rauni bayan an yi musu dukan kawo wuka.

Agefe guda kuma tawagar kungiyar Hamas karkashin jagoranci Khalil al-hayya ta isa birnin al-qahira na kasar Masar inda za ta gana da jarid Kushner manzon musamma na kasar Amurka  kan yarjejeniyar gaza da aka cimma.   

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted