Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar yamen sun kai wasu sabbin hare-hare a sansanonin sojin da kasar saudiya ke maraba musu baya a barin marib da tashar jirgin ruwa dake bahar maliya a garin mocha, a wani matakin na matsin lamba kan kasar saudiya adaidai lokacin da aka shiga wani sabon yanayi a yakin da ake yi.
Majiyar labaran sojojin kasar Yamen sun tabbatar da kai harin da kuma irin sakamakon da harin ya jawo, tace sojojin sun kai hari a wani gini na sojojin saudiya a garin mocha da yankin marib da makamai masu linzami kirar balistic da kuma jiragen sama marasa matuki .
Matsin lambar ya ci gaba da tsananta, a farkon watan Agusta sojojin kasar yamen sun kai hare hare da makami mai linzami da jiragen sama marasa matuki a sansanonin soji dake marib da hadaramauta wanda rahotanni suka ce an kashe akalla ma’aikata 30 da kasar saudiya ke marawa baya
Daga karshe wannan matakin soji yana wakiltar wani yunkur mafi karfi da sojojin kasar yamen ke yi na tilastawa kasar saudiya ta dage takunkumin da ta kakabawa kasar Yamen, wanda aka dade ana daukarta a matsayin kasa mafi talauci a kasashen larabawa, da kuma kawo karshen ta’addanci da take yi na tsawon lokaci