Yemen: Saudiyya Zata Biya Farashin Ta’addancinta Kan Kasar

Kakakin Rundunar Sojin Yemen ya bayyana cewa: Inkarin Saudiyya game da kai hari kan Yemen ba zai wanke ta daga munanan aniyarta ba Kakakin Rundunar

Kakakin Rundunar Sojin Yemen ya bayyana cewa: Inkarin Saudiyya game da kai hari kan Yemen ba zai wanke ta daga munanan aniyarta ba

Kakakin Rundunar Sojin Yemen, Birgediya Janar Yahya Sari’e, ya tabbatar da cewa: “Yunkurin maƙiya na Saudiyya na musanta hare-haren da suke kai wa Yemen, ba zai wanke su daga fuskantar mummunan sakamakon ayyukansu harin ba.”

A cikin wani rubutu da ya yi a dandalin “X”, Sari’e ya ce: “Yunkurin maƙiya na Saudiyya na musanta laifukan da suke yi da kuma cin zarafin al’ummar Yemen, ba zai wanke su daga mummunar sakamakon wadannan hare-haren wuce gona da irin ba, komai ƙoƙarin da suke yi na ɓoye gaskiyar lamari.”

Ya ƙara da bayyana cewa: Jirgin da ya kai hari gidan yarin tsakiya da ke gundumar Al-Hazm “ya tashi daga sansanin sojojin sama na Sarki Khalid da ke Khamis Mushait kuma bayan kai harin ya koma sansanin.”

Sari’e ya lura cewa: Gwamnatin Saudiyya ta kai hari gidan yarin tsakiya da ke birnin Al-Hazm, wato gundumar Al-Jawf, a ranar Litinin da ta gabata, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar fursunoni da baƙi masu ziyaza masu yawa, ciki har da yara da mata.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Saudiyya ke kai hare-haren sama kan wasu yankunan Yemen, ciki har da Ma’arib, Al-Jawf, Taiz, da Hodeidah, don tallafawa da kuma ƙarfafa tarin sojojin Saudiyya a ƙasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted