Jami’in Sojin Iran: Iran Ta Canza Yanayin Yaki Da Makiyanta

Mataimakin Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Iran ya bayyana cewa: Canza yanayin yaki da Iran ta yi ya wuce tsammanin abokan gaba Mataimakin Babban Hafsan Hafsoshin

Mataimakin Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Iran ya bayyana cewa: Canza yanayin yaki da Iran ta yi ya wuce tsammanin abokan gaba

Mataimakin Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Iran, Birgediya Janar Kioumars Haidari, ya tabbatar da cewa: Makiya ba su taba tunanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta iya canza yanayin yaki da kuma fadada fagensa zuwa wani mataki na yanki ba.

Ya bayyana cewa: Mashigar Hormuz wani muhimmin wuri ne na dabaru da kuma muhimmanci a yankin, wanda ke da tasiri mai yawa kan yanayin yanki da na duniya.

Ya kara da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ta hanyar amfani da dabarunta, ta samu damar yin tasiri mai ma’ana a fannin tattalin arziki na duniya.

Birgediya Janar Haidari ya sake nanata cewa: Makiya ba su taba tsammanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta iya canza daidaiton yaki da kuma fadada fagen yakin zuwa wani mataki na yanki ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted