Kwamandan Rundunar Sojin Kasa ya sanar da cewa: Rundunar ta shirya tsaf don tunkarar kowace barazana
Kwamandan Rundunar Sojojin Kasa, Birgediya Janar Ali Jahan-Shahi, ya jaddada cewa: Barazanar da makiya suke yi kan Jamhuriyar Musulunci, ko da kashi daya cikin dari ce, dukkan sojojin Iran, sun shirya tsaf don tunkarar duk wata barazana a kowane hali.
Birgediya Janar Jahan-Shahi ya bayyana cewa: Sojojin Kasa na ci gaba da kasancewa a kan iyakokin kasar, suna aiki don kare iyakokin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da cikakken shiri.
Kwamandan Rundunar Sojojin Kasa ya dauki kasancewar Sojojin Kasa a cikin ramukan kariya a matsayin tushen tabbatar da zaman lafiyar al’ummar Iran da kuma hana makiya gudanar da hare-haren wuce gona kansu, yana mai karawa da cewa: “Wannan karfin tsaron jami’an Iran ya kasance yana nuna cewa Sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran suna nan a koyaushe cikin shiri dauke da ruhin jihadi don kare kasarsu da ‘yancin kai.”
Birgediya Janar Jahan-Shahi ya jaddada wajibcin kiyaye Shirin kasa daga duk wata barazana da za a fuskanta nan gaba, yana mai cewa: “Kamar yadda Marigayi Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci da ya yi shahada ya ce: Barazanar kashi daya cikin dari, barazana ce ga sojojin kasa da suke daukarta da muhimmanci, saboda haka, sojojin Iran sun shirya tsaf don tunkarar duk wata barazana a kowane hali.”