Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik Badruddeen Huthi ya bayyana cewa tun bayan hare haren 11 ga watan satumban shekara ta 2001 ne kasashen yamma, tare da fakewa da sunan yaki da ayyukan ta’addanci suke farwa kasashen musulmi da sunan yaki da ayyukan ta’addanci, da kuma manufar tsorata da wasu kasashen wadanda suka mika kai ga rewsu inda kuma suke kwasar arzikin da kasashen suka mallaka don amfanin kansu.
Huthi ya bayyana haka ne ajiya Asabar a lokacinda ya ke gabatar da jawabi, wanda kuma aka watsa kai tsaye ta tashar talabijin ta kungiyar wato ‘Almasirah’ a jiya Asabar da yamma.
Ya kuma kara da cewa abin bakin ciki kuwa shi ne yadda wasu kafafen yada labarai na kasashen musulmi suka mika kai ga farfagandar wadannan kasashe, har suka fara goyon bayan kasashen na yamma suke kuma tayasu a yaye yaken da suka sanyawa suna yaki da ayyukan ta’addanci amma a kasashen musulmi kadai.
Shugaban na kungiyar Ansarullah ya bayyana cewa hare haren da Amurka da kawayenta na kasashen yamma suka kaiwa kasashen Afganistan Iraki da kuma Siriya duk suna cikin jerin wannan shirin, sannan manufofin wadannan kasashe shi ne kara karfin ikonsu a kan kasashen musulmi , da kuma tilasta masu mika kai ga bukatunsu.
Sayyid Abdulmalik badrudeen Huthi ya kammala da cewa, bayan haka wadanda kasashen sun shiga ikin barazana da tsoratar da kasashen musulmi don kara mika kai ga bukatunsu.
Amma akwai wasu kasashen musulmi wadanda suka tsaya a kan duga dugansu suka ki mika kai ga bukatun wadannan kasashen. Ya ce turjiya da kuma fuskantar wadannan kasashe ya zamawajibi ga kasashen musulmi. Don kare kansu dakuma tabbatar da cewa dukiyoyinsu sun zama masu amfani a garesu.