Shugaban kasar Senegal Yana Shirin Kafa Sabuwar Jam’iyyar Siyasa

Shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye yana Shirin kaddamar da sabuwar jam’iyyar siyasa bayan da sabani a tsakaninsa da Fira Minista Ousmane Sonko ya kara

Shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye yana Shirin kaddamar da sabuwar jam’iyyar siyasa bayan da sabani a tsakaninsa da Fira Minista Ousmane Sonko ya kara fadada.

Wannan matakin na shugaban kasar yana zuwa ne gabanin kaddamar da zabukan kananan hukumomi da za  ayi ba da jimawa ba da kuma kwaskwarimar da aka yi wa tsarin mulkin kasar.

Magoya bayan shugaban kasar ta Senegal ne su ka sanar da cewa tuni ya fara Shirin kaddamar da sabuwar jam’iyya,kuma tuni ya bai wa babbar mai ba shi shawara Aminat Toure umarnin ta jagoranci sabon yunkurin kafa sabuwar  jam’iyyar.

Idan aka kafa sabuwar jam’iyyar zai zama an gama raba gari a tsakanin shugaban kasar da kuma Fira ministansa.

Tun bayan da aka rantsar da shi a matsayin sabon shugaban kasar Faye, yake ci gaba da zama a jam’iyyar da take Mulki a kasar ta “Pastef”,to amma aka ci gaba da samun sabani a tsakaninsa da Fira minista.

Sonko ya zama shugaban majalisar dokokin kasar, wanda kuma ya jagoranci kwaskwarimar da aka yi wa  tsarin Mulki da ya rage karfin shugaban kasa. An kuma sauya dokar da ta mayar da shugaban kasa zama shugaban jam’iyya.

Ya zuwa yanzu dai ba a sanar da lokacin yin zabukan kananan hukumomin ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted