Jaridar Politico ta dauki labarin da yake cewa; kungiyar “Nato” tana karfafa bangarenta dake daura da Rasha domin yiyuwar barkewar fada a tsakaninsu.
Jaridar ta ce hakan tana faruwa ne a daidai lokacin da mambobin kungiyar suke son rage dogaro da Amurka.
Haka nan kuma jaridar ta ambaci cewa; Abinda yake faruwa shi ne kokarin da kasashen turai suke yi domin karfafa bangarensu na gabas, domin fuskantar kalubalen da suka zaton cewa Washington ba za ta iya fuskanta ba.
Wani sashe na labarin da jaridar ta buga ya ambaci cewa, rashin yarda da juna a tsakanin bangarorin biyu ya kara kamari ne sanadiyyar yaki da Iran,musamman bayan da shugaban kasar Amurka ya yi barazanar yin nazari akan ci gaban kasar a cikin kungiyar. Trump din dai ya bayyana hakan ne saboda yadda ya zargi kasashen Nato da kin taimaka wa Amurka a yakin da take yi da Iran.
A cikin kwanakin bayan nan dai kasashen Nato da Rasha sun kara yi wa juna barazana dake haifar da fargaba akan cewa fada zai iya barkewa a tsakaninsu.