Miliyoyin Mutane Sun Halarci Jana’izar Imam Khaminaei A Qom Bayan Tehran

Miliyoyin mutanen Iran da kuma wasu daga kasashen waje ne suka halarci sallar Jana’izar Imam Sayyid Aliyul Khaminaei a masallacin Jamkaran dake wajen birnin Qom

Miliyoyin mutanen Iran da kuma wasu daga kasashen waje ne suka halarci sallar Jana’izar Imam Sayyid Aliyul Khaminaei a masallacin Jamkaran dake wajen birnin Qom na ilmi a yau Talata.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, Ayatullahi Abdullahi Jawadi Amuli ne ya jagoranci sallar jana’izar Imam Khaminaei da iyalansa inda miliyoyin mutane suka halarta.

Sannan bayan sallar an raka jana’izar zuwa hubbaren Fatimah Ma’asuma daga cikin birnin Qom inda.

Labarin ya kara da cewa turuwan `mutane sun fara isa masallacin ne tun jiya saboda halartar jana’izar bayan sallar Asubaha. Sannan da dama sun taka da kafafuwansu zuwa masallacin saboda halartar jana’izar.

A ranakuna Lahadi da litinin ne aka ajiye gawakin Imam Khaminaei da Iyalansa a Musallah na Tehran kafin a yi masu salla a ranar Litinin. Banda birnin Qom gobe Talata da safe za’a kai shi zuwa biranen Najaf da Karbala na kasar Iraki. Sai kuma bayan Iraki za’a maida shi mahaifarsa birnin Mashad dake arewa maso gabacin kasar Iran don sanya shi a makwancinsa na karshe.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted