Shugaban Kasar Amurka Ya Isa Turkiyya Don Halattan Taron Kungiyar Tsaro Ta NATO

Shugaban kasar Amurka Donal trump ya isa kasar turkiyya don halattan taron kungiyar tsaro ta NATO ta, inda bayan isarsa ya fadawa shugaban kasar turkiyya

Shugaban kasar Amurka Donal trump ya isa kasar turkiyya don halattan taron kungiyar tsaro ta NATO ta, inda bayan isarsa ya fadawa shugaban kasar turkiyya Rajab Tayyib Urdogan kan cewa, mai yuwa ya sayar masa jiragen yaki samfurin F-35 wadanda suka dade suna cece kuce a kan hakan, bayan da kasar Turkiyya ta saye garkuwan makamai daga kasar Rasha.

Tashar talabijan ta Al-Mayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa, wannan shi ne taron shuwagabannin kungiyar ta farko bayan yakin da Amurka da HKI suka kaiwa kasar Iran a farkon wannan shekara. A cikin yakin Ramadan wanda kasashen biyu suka dorawa kasar Iran an kakkabo jiragen yakin Amurka da dama daga ciki har da jirgin yaki kirar Amurka samfurin F 35.

Tun shekara ta 2019 ne kasar Turkiyya take bin Amurka don ta sayar mata jirgin yaki Samfurin F 35, amma taki amincewa saboda kasar Turkiya ta sayi garkuwan makamai samfurin S-400 daga kasar Rasha.

Shugaba Trump ya bukaci taimakon kasashen kungiyar tsaro ta NATO a yakin da ya dorawa kasar Iran amma sun ki amincewa da bukatarsa.

Ana saran shuwagabannin kungiyar zasu tattauna kan shirin Trump na kwace yankin Greenland na kasar Nethalanda a wannan taron, da kuma batun yaki a Ukrain.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted