Shugaban haramin Imam Hussain (a) a birnin Karbala na kasar Iraki ya bada sanarwan cewa, Al-Kabalaei ne zai jagoranci sallar Jana’izar Imam Khaminaei a birnin Karbala, a gobe Laraba da yamma, .
Kamfanin dillancin labaran Tasnim news na kasar Iran ya nakalto majiyar ofishin Ayatullahi Sistani na cewa Babban malami kuma marja’I ba zai iya yin salla wa Imam Khaminaei Shahid da iyalansa ba saboda yanayin da yake ciki na rashin lafiya da tsufa. Ya kuma kara da cewa, iyakan Imam Khaminaei sun kuma amince da hakan.
Sojojin Amurka da HKI ne suka kashe Imam Sayyid Aliyul Khaminaei da iyalansa a ranar farko nay akin kwanaki 40da suka dorawa JMI wanda yake jagoranta kimani shekaru 40 da sukagabata.
Miliyoyin mutane a kasashen Iran da Iraki ne zasu halarci jana’izar Imam Khaminaei a kasashen biyu. Ana saran za’a kaishi birnin Mashad na araewa maso gabatcin kasar Iran a jibi Alhamis don yi masa sallah ta karshe da kuma binneshi a kusa da hubbaren Imam Aliyu bin Musa Arrida (a).