Ministan harkokin wajen Jamhuriyar musulunci Dr. Abbas Arakci ya bayyana cewa; A karkashin nagare na 13 na takardar fahimtar juna a tsakanin Iran da Amurka, an bayyana cewa;matukar ana yi wa Iran barazana, to kuwa ba za a hau teburin tattaunawar karashe ba.
Sayyid Abbas Arakci wanda ya halarci jana’izar jagora shahidi ya kuma ce; Miliyoyin mutanen Iran sun fito cikin hadin kai domin girmama Ayatullah Khamenei da kuma girmama ayyukan da ya bari, don da su da sojojin kasar da kuma mu, ba za mu taba amincewa da duk wata barazana ba.
Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma yi Ishara da cewa:
” A karkashin nagare na 13 na takardar fahimtar juna a tsakanin Iran da Amurka, an bayyana cewa;matukar ana yi wa Iran barazana, to kuwa ba za a hau teburin tattaunawar karashe ba.”