Minsitan Harkokin Wajen Rasha Sergei Lavrov Zai Ziyarci Nijar A Gobe Laraba

Minsitan Harkokin Wajen Rasha SergeiLavrov zai ziyarci Jamhuriyar Nijar a gobe Laraba. Lavrov zai je Nijar ne don halartar taron ministocin harkokin waje karo na

Minsitan Harkokin Wajen Rasha SergeiLavrov zai ziyarci Jamhuriyar Nijar a gobe Laraba.

Lavrov zai je Nijar ne don halartar taron ministocin harkokin waje karo na biyu tsakanin Rasha da Kawancen Kasashen Sahel wato (Mali, Nijar da Burkina Faso).

A cewarsa, tawagar Rasha za ta yi la’akari da sakamakon tattaunawar da ta yi da Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka, Mahamad Ali Youssouf, da nufin kulla dangantaka mai karfi tsakanin kasashen na Sahel Uku da Tarayyar Afirka.

Wannan shi ne ziyarar aiki na farko wanda ministan harkokin wajen  Rashar zai kai nahiyar Afrika da nufin karfafa alaka da nahiyar a bangarori da dama saboda amfanar juna.

Kafin hakan dai minsitan harkokin wajen rasha ya bayyana tattaunawarsa da Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka, Mahamad Ali Youssouf, a matsayin “mai ma’ana da armashi.”

 A yayin tattaunawar, bangarorin biyu sun amince su gudanar da shawarwarin siyasa na shekara-shekara.

A cewar Ministan Harkokin Wajen Rasha, wannan tattaunawar ta zama tushen dangantaka tsakanin Rasha da Tarayyar Afirka.

Ministan Harkokin Wajen Rasha ya tabo matsalolin tsaro da ke addabar  yankin Sahara da Sahel, da Kahon Afirka, da kuma kasar  Sudan, da Sudan ta Kudu, da Libya, inda ya bayyana cewa Moscow za ta ci gaba da tallafawa abokan huldarta na nahiyar  Afirka wajen warware wadannan rikice-rikice.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted