Miliyoyin Mutane A Birnin Qum Suna Yin Bankwana Da Jagora Shahidi

A yau Talata miliyoyin mutanen birnin Qum su ka fito kwansu da kwarkwatarsu na layi mai tsawon kilo mita 7 daga masallacin Jamkaran zuwa haramin

A yau Talata miliyoyin mutanen birnin Qum su ka fito kwansu da kwarkwatarsu na layi mai tsawon kilo mita 7 daga masallacin Jamkaran zuwa haramin Fatima Ma’asumah ( a.s).

Tashar talabijin din al’alam ta ambaci cewa; Ayatullah Jawad Amuli ne ya yi wa jagoran sallar jana’aza a masallacin Jamkaran tun da jijjifin safiyar yau Talata.

Baya ga birnin Qum, wasu miliyoyin mutane da su ka fito daga birane mabanbanta na kasar suna cikin masu halartar  jana’izar ta jagora shahidi.

Mafi yawancin mahalarta jana’izar suna dauke da hotunan jagora shahidin da kuma tutocin Iran, da na Ashura.

A jiya Litinin ne dai mutanen Tehran su ka yi bankwana da na karshe da jagoran juyin musuluncin Ayatullah Sayyid Ali Khamenei wanda ya yi rayuwa tare da su a tsawon shekarun juyi. An fara zaman makokin Jagora shahidin ne tun ranar Juma’a da wakilan kasashen waje su ka yi girmamawa ta karshe ga Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.

Daga ranar Asbar kuwa al’ummar kasar ta Iran ce su ka halarci jana’izar ta jagoran juyi.

Ana sa ran cewa daga gobe Laraba za a kai gawar shahidin zuwa kasar Iraki, a hubbaren Imam Ali (a.s) a birnin  Najaf da kuma na Imam Hussain ( a.s) dake birnin Karbala.

Ya zuwa yanzu dai fiye da mutane miliyan 25 ne su ka halarci jana’izar ta jagora shahidi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted