Iran Ta Yi Watsi Da Rahoton Da UAE Ta Mikawa Hukumar Zirga Zirgan Jiragen Ruwa Ta Duniya (IMO)

Gwamnatin kasar iran ta yi watsi da rahoton da UAE ta mikawa hukumar zirga zirgan jiragen ruwa ta duniya wato (Council of the International Maritime

Gwamnatin kasar iran ta yi watsi da rahoton da UAE ta mikawa hukumar zirga zirgan jiragen ruwa ta duniya wato (Council of the International Maritime Organization (IMO) dangane da mashigar ruwa ta Hurmuz ta kuma kara da cewa UAE ta yi haka ne don siyasa da kuma matsin lamba daga wasu kasashe. Banda haka rahoton bai da wani kima a wajenta.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran Tehran tana bada wannan bayanin ne a yau Talata, a wani sakon maida martani da ta aikewa hukumar IMO tana cewa, zarge zargen da Abu Dabi ta gabatar bai da wani kima a mahanyar sharia, kuma akwai bangaranci da rashin dacewa da kalaman da aka yi amfani da su a cikin korafin.

Iran ta ce, a rahoton da UAE ta gabatarwa, IMO, wanda kuma ya sami goyon bayan wasu kasashen yankin guda 8, sun sanya laifi a kan wanda aka yiwa laifi, sannan sun manta da asalin abinda ya kawo matsalolin tsaro a yankin yammacin Asiya.

Ta ce yakin da Amurka da HKI suka dorawa kasar Iran shi ne ya haddasa dukkan matsalolin tsaro a cikin tekun Farisa da tekun omman da kuma mashigar ruwa ta Hurmuz, kafin yakin babu wata matsalar tsaro a zirga zirgan jiragen ruwa a wadan nan yankuna. Amma rahoton kasar UAEA bait abo wannan batun kwata-kwata.

Daga karshe gwamnatin kasar Iran ta yi kira ga hukumar IMO ta yi nazarin al-amuran da suka zo cikin rahoton ta kuma dauki matakan da suka dace cikin adalci da hangen nesa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted