Shugaban hukumar bada agajin gaggawa a jihar Naija na tarayyar Najeriya NSEMA ya basa sanarwan cewa yawan mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar ambaliyar ruwa a ranar Alhamis data gabata a karamar hukumar Mokwa ya kai 151 bayan an sake gano karin gawakin mutane 36.
Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto Abdullahi Arah yana cewa banda wadanda suka rasa rayukansu mutane 11 ne suka ji rauni. Sannan mutane 3018 suka kauracewa gidajensu sanadiyyar ambaliyar ruwa bayan ruwan sama na sa’oii masu yawa.
Arah yace gidaje 503 ne suka rushe a jihar sannan wasu 265 suka lalace. Banda haka akwai gadoji biyu da hanyoyi biyu wadanda ruwan ya sharesu.