Dubban ‘yan gudun hijirar Sudan ne ke zaune a dajin da ke kusa da kan iyakar Habasha da Sudan bayan da suka tsira daga hare-haren da wasu ‘yan bindiga suka kai musu kan sansanonin su da Majalisar Dinkin Duniya ta samar musu a cikin kasar Sudan.
A zantawarsu da wakilin gidan talabijin na Al-Jazeera, ‘yan gudun hijirar sun bayyana cewa; Kimanin ‘yan gudun hijira 7,000 ne suka bar sansanonin kuma kusan 3,000 har yanzu suna rayuwa a cikin dajin tare da dabbobin daji kamar kuraye, kunamai da macizai.
Anata bangaren hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce: Kimanin mutane dubu ne suka tsere daga sansanonin ‘yan gudun hijira sakamakon hare-haren wuce gona da iri da suke fuskanta.
Tun a tsakiyar watan Afrilun shekara ta 2023, sojojin Sudan karkashin jagorancin Janar Abdul Fattah al-Burhan da kuma dakarun kai daukin gaggawa karkashin jagorancin Muhammad Hamdan Dagalo (Hemedti), suka kaddamar da yakin da ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 15,000 tare da raba kimanin miliyan 10 da muhallansu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.