Ali Akbar Vilayati mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aya. Khaminae ya bayyana cewa, yenci da kuma zaman lafiya da tsaron JMI yana da matukar muhimmanci ga kasar Iran.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Wilayati yana fadar haka a lokacin da yake ganawa da Ammar Hakin shugaban Jam’iyyar Hikma na kasar Iraki wanda yake ziyarar aiki a nan Iran a yau Lahadi.
Wilayati ya kara da cewa kasashen Iraki da Iran suna da dangantaka mai muhimmanci tsakaninsu wanda ya hada da na addini da al-adu ga kuma makobtaka.
Yace Iran tana jin dadin ganin Iraki tana samun ci gaba da kuma zaman lafiya mai dorewa a karkashin jagorancin malaman addini tare da hadin kai da dukkan mutanen kasar.
A na shi bangaren Sayyid Ammar Hakim ya bayyana cewa kekyawar Jagorancin da JMI take da shi ya daukaka kasar, haka ma sojoji da mutanen kasar sun hada kai don ganin bayan HKI a cikin yakin kwanaki 12 da ya gabata.
Ya ce: A karon farko tun bayan kafa HKI shekaru 76 da suka gabata, JMI ce ta ragargara HKI wanda babu shakka a cikinsa. Kuma wannan ya fidda kasar Iran a duniya.