Wata Tawagar Amurka Ta Je Nijar Domin Tattaunawa Kan Shirin Janye Sojojin Amurka

Wata tawagar manyan jami’an Amurka ta isa birnin Yamai domin tattaunawa kan shirin janye sojojin Amurka da gwamnatin Nijar ta bukata, kamar yadda ma’aikatar tsaron

Wata tawagar manyan jami’an Amurka ta isa birnin Yamai domin tattaunawa kan shirin janye sojojin Amurka da gwamnatin Nijar ta bukata, kamar yadda ma’aikatar tsaron Nijar ta sanar a ranar Laraba.

Ministan tsaron Nijar Janar Salifou Modi ne ya karbi tawagar ” ta Pentagon karkashin jagorancin Christopher Maier, mataimakin sakataren tsaro na ayyuka na musamman da kananan rikice-rikice a ranar Laraba.

Tawagar ta gabatawa Nijar wani daftari wanda za’a tatattaunawa da kwararun sojojin Nijar kan shirin janyewar sojojin na Amurka a cikin tsari.

Wannan shi ne “taron farko a hukumance” tun bayan da gwamnatin Nijar ta yi Allah wadai da yarjejeniyar hadin gwiwa da sojojin da aka kulla da Amurka a watan Maris.

A tsakiyar watan Afrilu ne Amurka ta amince ta janye sojojinta da aka tura a kasar domin yaki da ta’addanci.

A kwanan dai Firaiministan Nijar, Ali Mahaman Lamine Zeine ya yi wasu zafafan kalamai a kan alakar kasarsa da Amurka kan batun yanke dangantakar soji tsakaninsu, a wata hira da ya yi da Washington Post a ranar Talata.

Zeine ya ce mataimakiyar Sakataren Harkokin Wajen Amurka a Afirka, Molly Phee, wacce ta jagoranci ziyarar ta tawagar, ta yi barazanar sanya wa birnin Yamai takunkumai idan Nijar ta rattaba hannu kan yarjejeniyar sayar da sinadarin uranium da take hakowa ga Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments