Wasu Yan Saudiya Sun Mutu Sakamakon Harin Da Yamen Ta Kai

wasu mutanen saudiya sun mutu wasu kuma sun jikkata sakamkon harin da dakarun kasar Yamen suka kai saudiya

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar Yamen sun kaddamar da hari da makami mai linzami mai cin dogon zango da jirage marasa matuki a sansani ajiye makamai ga sojojin haya da kasar saudiya ke mara wa baya a yankin Mokha dake lardin Taizz da kuma sansaninsu na tadwin dake lardin Ma’arib

Kakakin sojin kasar Yamen birgediya janaral yahaya Saree shi ne ya fitar da bayani a sanarwa da yayi a jiya talata inda yace farmakin ya kunshi amfani da makami mai linzami na Ballistic da kuma jirage marasa matuki kuma sun samu inda aka hara da ya hada da cibiyar da take bada umarni

Haka zalika Saree yace harin ya kashe mutane da dama da kuma jikkata wasu na daban ciki har da yan kasar saudiya, kuma harin yana zuwa ne bayan da dakarun sojin kasar suka kaddamar da hare-hare kan dakarun da saudiya ke marawa baya a karo na biyu a jere

A ranar litinin da ta gabata dakarun sojin kasar yamen sun kai hari kan sojojin haya da saudiya ke marawa baya da ake kira da suna dakarun tabbatar da tsaro na Shabwa a garin bayhan dake yankin kudu masu gabashin lardin shabwa kamar yadda majiyar labarai ta cikin gida ta bayyana kuma akalla sojan haya guda  ya mutu wasu da dama kuma  sun jikkata

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted