Aragchi: Tir Da Faransa Kan Zargin Iran Da Take Hakkin Bil’adam

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi tir da gwamnatin kasar Faransa kan munafurcin ta kan abinda ya shafi kare hakkin bil’adama. Kamfanin

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi tir da gwamnatin kasar Faransa kan munafurcin ta kan abinda ya shafi kare hakkin bil’adama.

Kamfanin dillancin labaran Mehrnews Agenci na kasar Iran ya nakalto Arachi yana fadar haka a shafinsa na X ya kuma kara da cewa, Faransa da sauran kasahe 25 na tarayyar Turai da kuma kungiyar EU munafukai ne a lokacinda suke kiran Iran ta kawo karshen kashe wadanda suka kashe Iraniyawa a rikice rikicen na farkon wannan shekarar, sannan sun rufe idanunsu daga kallon goyon bayan da suka bawa HKI tana kashe Falasdinawa a Gaza, da kuma hare haren da Amurka da HKI suka kai kan kasar Iran. Inda suka kashe dubban mutane.

Ministan ya kara da cewa, kasar Faransa da sauran kasashen Turai sun rasa mutuncin fadawa wata kasa a duniya ta kare hakkin bil’adama tun lokacinda suke goyon bayan HKI ta kashe falasdinawa fiye da 73k a gaza da kuma hare haren da Amurka da HKI suka kai kan kasar Iran dun haka wadan nan kasashe basu cancanci a sauraresu ba, idan an zo magana kan kare hakkin bil’adama.

A cikin yan kwanakin da suka gabata ne ma’aikatar harkokin wajen kasar Faransa a madadin sauran kasashen turai 25 da kuma kungiyar EU suka fitar da bayani dangane da kissan yan ta’adda a kasar Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted