Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya shiga jirgin shugaban kasa mai suna Airforce One a idon jama’a a lokacinda aka kammala taron NATO a kasar Turkiyya a watan da ya gabata, amma yan mintoci bayan shigarsa jirgin sai aka fito da shi ta kasa ya kuam wata motar daukan abinci a tashar jiragen sama na Ankara zuwa wani dan karamin jirgin da ke tsaye kusa da Airforce One, ya tashi ya isa kasar Burtania saboda kaucewa tsaron da kuma barazanar kisa daga magoya bayan kasar Iran.
A karshen watan Fabrayru ne Trump da HKI suka farwa kasar Iran da yaki, suka kuma bayyana cewa bata da mafita in bada mika kai.
Amma bayan yaki na watanni,an gano cewa kasashen biyu basu da karfin sauya gwamnati a kasar Iran duk tare da cewa sun kashe shuwagabannin kasar da dama.
Tun daga lokacin ne Trump yake kaucewa makaman kasar Iran wanda mai yuwa ta rutsa da shi, a cikin jirgin fadar shugaban kasa dai akwai sauran manya manyan jami’an gwamnatinsa wadanda suka hada da Maco Rubio da sauransu. Wadanda ya saida ransu shi ya tsere da wani karamin jirgi.