Iran: Hurmuz Zata Ci Gaba Da Halin Da Take Ciki Har Zuwa Lokacinda AKa Cika Sharuddan Kasar
Hukuma ta musamman mai kula da mashigar ruwa ta Hurmus a nan Iran ta bada sanarwan cewa mashigar zata ci gaba da kasancewa a rufe har zuwa lokacinda Amurka zata amince da sharuddan gwamnatin kasar na bude ta.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto hukumar na fadar haka, ta kuma yi kira ga mutane kada mutane su saurari karyayyakin da gwamnatin kasar Amurka take yadawa kan cewa mashigar a bude take, ta kuma sanyasu cikin hatsari na rasa dukiyoyinsu ko kuma har da rayukansu.
“The Persian Gulf Strait Authority (PGSA) ta bayyana haka a shafinta na X a jiya Laraba ta kuma kara da cewa saw da dama gwamnatin Amurka ta sanya jirage masu yawa cikin hatsari bayan sun yada labaran karya na bude mashigar amma suka fada cikin tarko suka kuma yi asarari masu yawa.
A ranar 28 ga watan Fabrayru ne Amurka da HKI suka farwa kasar Iran da yaki, suka kashe mutane da dama daga ciki har da Jagoran juyin juya halin musulunci Imam sayyid Aliyul Khamania. (q).
An tsagaita wuta a ranar 8 ga watan Afrilu aka rattaba hannu kan takardun sulhu Trump ya saba masu. Sai Iran ta sake rufe mashigar.
Daga cikin sharuddan akwai dauke mata takunkuman tattalin arziki, sake kudadenta da Amurka ta tsare amincewa da ikon Iran a kan wannan mashigar.