Pezeshkian: Iran Ba Ta Sabawa Dokokin Kasa Da Kasa Ba

Shugaban Kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta aikata abin da saba wa tsarin dokokin kasa da kasa Shugaba kasar Iran

Shugaban Kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta aikata abin da saba wa tsarin dokokin kasa da kasa

Shugaba kasar Iran Masoud Pezeshkian, a wata tattaunawa ta wayar tarho da Fira Ministan Japan Sanae Takaichi, ya bayyana cewa: Iran ba ta taɓa yin wani abu a waje da tsarin dokokin ƙasa da ƙasa ba kuma koyaushe tana ƙoƙarin inganta dangantakarta da ƙasashen da ke maƙwabtaka da ita.

Kamfanin dillancin labaran “IRNA” ya ruwaito cewa: Shugaba Pezeshkian, a lokacin kiran a ranar Laraba, ya nuna godiyarsa ga ra’ayoyin Japan masu kyau game da buƙatar kawo ƙarshen yaƙin. Ya jaddada cewa Iran ba ta taɓa neman rashin tsaro a yankin ba, sai dai Amurka da ‘yan Sahayoniyya ne ke da alhakin wargaza yankin ta hanyar kai hare-hare kan Iran, kisan gillar da aka yi wa Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei (Allah ya yi masa rahama), da kuma shahadar fararen hula da dama—ciki har da yara ‘yan makaranta a birnin Minab (kudancin Iran)—da kuma lalata kayayyakin more rayuwa na fararen hula.

Shugaban ya kuma jaddada cewa: Iran ba ta yi wani abu a waje da dokokin kasa da kasa ba, kuma koyaushe tana kokarin karfafa dangantakarta da kasashen makwabta, yana mai bayyana fatansa na cewa kokarin diflomasiyyar Japan da nufin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin zai haifar da sakamako mai kyau, tare da samun nasarar hana masu kai hari daga aikata laifuka da kuma kunna wutar yaƙe-yaƙe.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted