Kakakin Ma’aikatar Harkokin wajen Iran ya yi shagube ga Amurka cewa: Shin duniya tana komawa zamanin ” Tsohon Yankin Yammacin Amurka ce”?
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya yi tambaya ko duniya ta koma ga zamanin “Tsohon Yankin Yammacin Amurka ne” yadda rayuwa ta koma ta daji babu doka da Oda?
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Isma’il Baqa’i ya jaddada cewa: Ba zai yiwu a sake doka ko soke hukuncin kotu ta hanyar wallafa rubutu guda daya a Shafin yanar gizo ba- musamman bayan da wata hukumar shari’a ta kasa da kasa mai hurumi ta fitar da takardar kama wasu masu laifi daga bangaren ‘yan sahayoniyya dangane da laifukan da suka aikata a Gaza ba.
A cikin wani rubutu da ya yi a dandalin X, Baqa’i ya rubuta cewa: “Shin wannan tsari ne na duniya na ƙarni na 21, ko kuma zamanin tsohon Yammancin Dajin Amurka ne, inda jami’in ‘yan sanda da ya naɗa kansa ya bayar da sanarwar ja kuma a lokaci guda yana aiki a matsayin mai gabatar da ƙara, alkali, da mai aiwatar da hukunci?”
Ya ƙara da cewa: “Lokacin da wata hukumar shari’a ta duniya mai ƙwarewa ta bincika laifukan da aka aikata a Gaza kuma ta bayar da sammacin kama masu laifin yaƙin Isra’ila, ba zai yiwu a sake tsara doka ko a soke hukunce-hukuncen da aka riga aka yanke ba ta hanyar wallafa rubutu a shafin yanar gizo kawai ba.