Dubban daruruwan mutane, sun taru a hubbaren limami na 8 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s), don juyayin shahadarsa a rana irin ta yau a shekara ta 203h.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban cewa dukkan manya manyan tituna da suke shiga birnin Mashad babban birnin lardin Khurasan Razawi a cike suke da masu ziyara, wadanda suka taho daga wasura masu nisa don halartar makokin.
Hubbaren Imam Aliyu dan Musa Al-Reza (s) shi ne wuri na addinin mafi tsarki a kasar Iran, sannan bugu da kari a bana an sanya Imam Sayyid Aliyul Khaminaei da iyalansa wadanda suka yi shahada tare da shi a kusa da kabarin Imam Reza (a), wanda ya karawa juyayin na bana armashi.
A rana irin ta yau ce sarki Mamon dan Sarki Haruna Rasheed ya kashe Imam Reza (a) da guba bayan ya tilasta masa zuwa garin maru na lardin Khurasan a lokacin. Saboda sanya ido a kan al-amuransa. Kusa da shi.