Iran Ta Ya Allawadai Da Zancen HKI Na Mallakar Tuddan Golan

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fidda wani bayani wanda yake allawadai da bayanan HKI dangane da tuddan Golan na kasar Siriya da kuma kasar

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fidda wani bayani wanda yake allawadai da bayanan HKI dangane da tuddan Golan na kasar Siriya da kuma kasar falasdinu da ta mamaye.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto ma’aikatar na fadar haka a safiyar yau Alhamis, ta kuma kara da cewa hakan ya babawa dokokin kasa da kasa.

Har’ila yau bayanin ya kara da cewa, gwamnatin kasar Iran tana allawadai da gwamnatin kasar Colombia wacce ta bayyana amincewarta da samuwar HKI, da kuma mamayar da takewa kasashen Larabawa musamman a yankin yammacin Asia.

Bayanin ya kara da cewa dokokin MDD a fili sun bayyana cewa mamayar kasashen larabawan da HKI na gaza da yankin yamma da kogin Jordan da tuddan Golan na kasar Siriya duk basa bisa ka’ida. Kuma a cikin yan kwanakin da suka gabata majalisar ta bukaci a rusa dukkan gine ginen da yahudawan suka yi a kan yankuna falasdinawa da suka mamaye a yankin yamma da kogin Jordan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted