Rahotanni sun bayyana cewa sojojin isra’ila sun kai hari kan wani mutum akan babur kuma yayi sanadiyar shahadarsa har da wani yaro karami tare kuma da jikkata wasu na daban a yankin Gaza
Sojojin isra’ila sun kai wa wani mutum hari dake kan babur a sansanin yan gudun hijara na shaikh ridwan dake yammacin gaza a jiya jumaa, kuma an gano gawar wanda abin ya shafa mai suna hudaifa awad tare kuma da wadanda suka jikkata da aka kai su wani asibiti,
Haka zalika a jiya jumaa sojojin isra’ila sun bude wuta a nusairat da sansanin yan gudun hijira na bureij dake tsakiyar gaza inda falasdinawa da dama yan gudun hijira suka ji mummunan rauni, kuma an kai harin ne kan falasdinawa da suka tarwatse sakamakon kisan kare dangi da suke musu.
Ofishin majalisar dinkin duniya mai kula da daidaita ayyukan agaji ya ba da rahoton cewa a makon jiya isra’ila ta kai hari a sauran muhimman wurare da ke gaza, da ya jawo jikkatar fararen hula da dama da kuma lalata muhimman kayayyaki da kuma tilasta musu barin gidajensu da karfin tsiya