Jaridar Washington Post ta nakalto wasu jami’an gwamnatin kasar ta Amurka suna fadin cewa; Yawan sojojin Amurka da aka kashe a yaki da Iran sun haura wadanda ma’aikatar yakin kasar Pentagon ta sanar a hukumance.
A jiya Juma’a ne dai jaridar ta Amurka ta buga rahoton akan yawan sojojin da su ka halaka a yaki da Iran, tana mai cewa ma’aikatar yakin kasar Pentagon ta rage yawansu a sanarwar da ta rika fitarwa.
Jaridar ta nakalto wasu jami’an gwamnatin Amurka su 6 da suke da bayanai daga cikin ma’aikatar yakin ana asarar rayukan da sojojin Amurkan su ka yi. Majiyar ta ce akalla da kawai wasu Karin sojoji 4 da ba a shigar da su a cikin bayanai wadanda aka kashe ba.
A gefe daya ma’aikatar yakin ta Amurka ta sanar da majalisar dokokin kasar cewa ya zuwa yanzu yaki da Iran ya ci kudin da sun kai Dala Biliyan 43.6
Kafar watsa labaru ta “Blomberg” ta ambato majiyar ma’aikatar yakin tana cewa; Zuwa 3 ga watan Satumba 2026 yakin ya kara cin wasu kudaden da sun kai Dala biliyan 11.2. Haka nan kuma an ware wasu kudaden da sun kai dala biliyan 28.1 domin sayen albarusai da makamai. Sai kuma wasu dala biliyan 4.3 domin sauya kayan yakin da aka lalata.
A yayin zaman karshe da majalisar ta yi da ministan yakin Amurka Peter Brian Hegseth ya ce yakin ya ci kudin da sun kai Dala biliyan 37.5. Sai dai kuma an bayyana cewa daga wancan loakcin, a kowane wata yakin yana cin kudin da sun kai Dala biliyan biyu zuwa uku.