Ƙungiyar masu dauke da makamai a tsakiyar kasar Habasha, ta kashe akalla mutane 14 tare da sace wasu 10, a wani hari da ta kai a farkon wannan makon.
Wata kungiya mai zaman kanta da ke sa ido kan rikice-rikicen masu dauke da makamai da kuma wani shaida ne suka shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP faruwar lamarin.
Kasar wacce ita ce ta biyu mafi yawan al’umma a Afirka, na fuskantar barazanar kungiyoyi masu dauke da makamai da ke kalubalantar sojojin kasar a yankuna biyu mafiya yawan al’umma, wato Oromia da Amhara, yayin da sauran sassan kasar ke fuskantar rikice-rikice daban-daban.
Jami’ar kungiyar Jalale Getachew Birru ta ce mayakan kungiyar masu dauke da makamai da ake kira da Fano sun kai hari garin Walga, mai nisan kilomita 150 ta kudu maso gabashin babban birnin kasar Addis Ababa.