Rahotanni sun bayyana cewa kararrawar gargadi da aka kunna ta karade birnin riyad na kasar saudiya a daidai lokacin da dakarun sojin yamen ke harba makamai masu linzami a birnin da ma wasu yankunan a matsayin mayar da martani kan hare-haren da kasar saudiya ta kai musu.
Haka zalika kamar yadda kafafen yada labarai na kasar saudiya suka sanar an ji karar kararrawar gargadi a tashar jiragen ruwa ta Yanbu dake tekun red sea dake yammacin kasar saudiya, da kuma birnin khamis mushait da Jizan da abha dake kudu masu yammacin kasar saudiya.
A wani bangare kuma an kashe wani babban jami’in sojin kasar yamen a wani hari da kasar saudiya ta kai a garin kaboub dake kusa da mashigar babul mandab.
Janaral firaq muhsen al assar kwamandan bataliyar sojin kasar yamen ta farko an kashe shi ne tare da wasu masu bashi kariya guda 6 harin da saudiya ta kai, dakarun sojin kasar yamen sun sanar da manyan nasarori da suka samu a hare haren da suka kai a kan jiragen ruwan kasar saudiya a tekun red Sea,