Kwana daya bayan mutuwar masu hako ma’adanai a hannun jami’an tsaro na farin kaya ( Civil Defence) a birnin Minna na jihar Niger, mutane sun hau kan titi domin yin zanga-zangar nuna kin amincewa da abinda ya faru.
Wadanda su ka tsira daga hannun jami’an tsaron na farin kaya, sun bayyana yadda wahalar da su ka sha a lokacin da suke tsare saboda zama cikin kananan dakunan da babu wadatacciyar iska, da ya sa suke lumfashi dakyar.
Wani daga cikin wadanda su ka tsirar ya shaida wa manema labaru cewa; mun rika ihu da kururuwa suna neman taimako, sannan muna fada musu cewa wasu daga cikinmu suna mutuwa, amma ba su yard da abinda muke fada ba.”
Wani kuma cewa ya yi; mun ja hankalinsu akan cewa wasu daga cikinmu sun riga sun mutu saboda shakewa,amma babu wanda ya amsa mana.”
Abinda ya faru ya fusata mutanen birnin Minna, ya kuma haifar da bore, sannan kuma jami’an tsaro da su ka fito su ka bude wuta akan mutane tare da kashe wasu daga cikinsu.”
A yanzu an tura jami’an tsaro da dama akan titunan birnin Minna domin kwantar da hankali.