Trump Ya Hana Kafafen Yada Labarai Na CNN Shiga white House

shugaban Amurka ya hana kafafen yada labarai na cnn da politico shiga fadar white house

Donald Trump shugaban kasar Amurka ya hana kafafen yada labarai na CNN MS now da kuma politico shiga fadar white house don daukar rahoto saboda da zargin da yake musu na cewa suna yada labaran karya game da gwamnatinsa,

A cikin wani bayani da ya wallafa a shafinsa na truth social a jiyar juma’a yace ina alfahari in sanar cewa matakin ya fara aiki nan take na hana kafafen yada labarai na cnn da ms now da politico shiga fidar white house saboda basu da aiki sai yada labaran karya

Sai dai kafafen yada labaran sun mayar da martani game da barazanar ta trump din yayi inda jaridar politico tace  zamu ci gaba da daukar rahoto mai kyau kan fadar white house da kuma wadanda za su zo anan gaba, kuma zamu kare hakkokinmu na kwaskwarimar da aka yi tun farko daga duk wani mataki na takaitamu

Ita ma CNN ta ce muna da hakki karkashin kundin tsarin mulkin Amurka mu dauki rahoto ba tare da cutarwa ko yin katsalandam a alamuran gwamnati ba, don haka trump ya ciba da yin barazanar da yake yi,

Haka zalika kamfanin ms now ya mayar da martanin cewa tun a lokacin yakin neman zaben shekara ta  2016 trump yake ci gaba da sukarsu cewa suna yada labaran karya,wasu zarge-zargen sun sa an dauki  matakin shari’a a kansu har zuwa yanzu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted