Amurka Ta Ficce Daga Hukumar Kare Hakkin Bi’adama Ta MDD

Gwamnatin kasar Amurka ta fice daga hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD wato ‘The UN Human Rights Council’ bayan da hukumar ta tabbatar da cewa

Gwamnatin kasar Amurka ta fice daga hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD wato ‘The UN Human Rights Council’ bayan da hukumar ta tabbatar da cewa akwai shaidu isassun wadanda zasu tabbatar da cewa Amurka ta aikata laifukan yaki a Iran a hare hare guda biyu da suka kai a kasar.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka na cewa kasar ta fice daga hukumar saboda tana nuna kiyayya ga bukatun Amurka sannan tana goyon bayan wasu kasashe wadanda suke riya cewa suna wakiltan mutanensu.

Labarin ya kara da cewa hukumar ta fara taronta na 63rd a birnin Geneva a a ranar 7 ga watan Satumban shekara ta 2026 sannan zasu ci gaba da taron har zuwa ranar 7 ga watan Octoma mai zuwa.

Gwamnatin Amurka ta fice daga hukumar ce bayan da “Fact-Finding Mission ta kasa da kasa mai zaman kanta ta buga binciken da ta gudanar danganeda ayyukan ta’addanci wadanda sojojin Amurka suka aikata a yakin da baya bisa ka’ida da ta farwa Iran da shi a ranar 28 ga watan Fabrairy na wannan shekarar.

MDD tana goyin bayan binciken ta kuma bayyana cewa tana da hujjoji kwarara don amincewa sojojin Amurka sun aikata laifukan yaki a hare hare guda biyu da ta kai kan kasar, wadanda ake iya siffantasu da hare hare kan fararen hula.ko wuraren fararen hula.  Daga cikinsu akwai hare da makami mai linzami smfurin Tomahok wanda ya fada kan makarantar firamari ta shajaratu ttaiyiba na arewacin garin Minab a kudancin kasar kuma yayi sanadiyyar kashe yan makaranta 120. Da wasu malamansu.

Da biyu kuma wanda suka kai kan wani dakin wasanni a lardin Fars kusa da gidajen mutane inda suka kashe yan wasa 22 fararen hula har da yara kanana.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted