Abass Araqchi ministan harkokin wajen kasar iran ya mayar da martani game da zargin da takwaransa na kasar Faransa Jean-Noel Barrot yayi na zargin iran karya hakokin bil adam, inda ya caccaki faransa game da yin gum da baki da ta yi game da kisan yara yan makaranta da kasar amurka tayi
A wani bayani da ya wallafa a shafinsa na X Araqchi y ace kimani alummar algeriya miliyan daya da rabi ne kasar faransa ta kashe a lokacin yakin neman yanci , kasa da kashe daya cikin 10 ne birnin paris ya taskace su , kuma yaki bada hakuri kan laifukan da ya aikata zamanin mulkin mallaka, don haka yana da kyau ta daina kukan karya shiru da baki da kuka yi lokacin da amurka ta yi kisan gillan kan yara yan makaranta ma ya isheku
Araqchi yana ishara ne da harin da Amurka takai a ranar 28 ga watan fabareru kan makarantar shajare dayyibe a minab dake kudancin kasar iran,da yayi sanadiyar mutuwar yara 168 da suka hada da yan makaranta120 malamai 26 sama da mutane 110 kuma suka jikkata.
A ranar Alhamis da ta gabata kwamitin bincike da majalisar dinkin duniya ta kafa ya fitar da sakamako dake tabbatar da cewa lallai amurka ta aikata kisan gilla a harin da ta kai kan kasar iran, tana ishara ga harin kan mai uwa da wabi da yayi sanadiyar kare fararen hula masu yawa da suka hada da mummunan hari kan makarantar shajare dayyibe.