Gaza: Falasdinawa Da Dama Sun Yi Shahada Da Kuma Jikkata A Yankuna Mabanbanta Na Zirin Gaza

Sanadiyyar ci gaba da Hare-haren sojojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila a yankuna mabanbanta na zirin Gaza, an sami Karin shahidai da kuma wadanda su ka jikkata
shahidan Gaza

Sanadiyyar ci gaba da Hare-haren sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila a yankuna mabanbanta na zirin Gaza, an sami Karin shahidai da kuma wadanda su ka jikkata mafi yawancin a sansanonin ‘yan gudun hijira.

A sansanin ‘yan hijira dake kusa da masallacin “taqwa” a arewacin Gaza, wani Bafalasdine daya ya yi shahada yayin da wasu da dama su ka jikkata daga cikinsu har da kananan yara.

A yankin “Sheikh Ridhwan ma an sami wasu Falasdinawan da dama da su ka jikkata saboda hare-haren ‘yan sahayoniya da manyan bindigogi.

 Rahotanni daga yammacin birnin Gaza sun ce mutum daya ya yi shahada bayan da wani jirgi maras matuki ya kai hari a kan titin al-Rashid.

Haka nan kuma ‘yan sahayoniyar sun kai wasu hare-haren a yankunan gabashin Gaza da kuma garin Beit-Lahiya a arewacin Gaza.

A sansanin Nusairat an sami shahidi daya mai suna Karam Mus’ad bayan da ya sami  raunuka masu yada daga hare-haren ‘yan sayahoniya.

A jiya ma wasu Falasdinawa biyu sun yi shahada saboda raunukan da su ka samu a baya a yankin Khan-Yunus.

Kididdigar ma’aikatar lafiya ta Gaza ta c; Tun daga tsagaita wutar yaki a ranar 11 ga watan Oktoba zuwa yanzu, adadin shahidai ya kai 1386,wadanda su ka jikkata kuwa sun kia 4,784. Har ila yau an iya fito da wasu shahidai 831 daga karkashin baraguzai da sojojin sahayoniya su ka rusa gidaje da mutane aciki a lokacin yaki.

Daga oktoba 2023 zuwa yanzu jumillar shahidai sun kai 73,821, sai wadanda su ka jikkata su 174,879.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted